fbpx
Sunday, April 18
Shadow

An yi ta karshe, Ba za’a sake satar Dalibai ba>>Shugaba Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa sace‘ yan mata da aka yi a ranar Juma’ar da ta gabata daga Makarantar Sakandaren Kimiyyar ’Yan Mata ta Gwamnati sake Jangebe, zai zama na karshe.

An kara jaddada bayanin Shugaba Buhari a ranar Lahadi ta hannun Ministan Sufurin Jiragen Sama, Sen. Hadi Sirika, wanda ya jagoranci wata babbar tawaga ta gwamnatin tarayya don jajantawa wa mutane da gwamnatin Zamfara.

Ya ce gwamnatin tarayya ta kirkiro sabbin matakai wadanda za su kawo karshen dukkan nau’ikan aikata laifuka a cikin kasar nan.

Sauran mambobin tawagar sun hada da Ministan Harkokin ’Yan sanda, Alhaji Maigari Dingyadi, Ministan Harkokin Jin Kai da Kula da Bala’i, Hajiya Sa’adiya Umar-Faruk da Ministan Harkokin Mata, Misis Pauline Tallen.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *