fbpx
Sunday, March 7
Shadow

Satar Tukunyar Abinci yayi sanadin mutuwar mutane 4 a Abuja

An zargi wasu masu gwangwan da laifin kashe wata mata me ciki a babban birnin tarayya,Abuja.

 

Bayan bacewar tukunyar girkinta, matar ta zargi masu aikin gwangwan din da cewa sune suka sace mata tukunyarta.

 

Anan cece-kuce ya kaure har ta kai ga masu kwankwan din sun cakawa matar wuka kuma ta mutu.

 

Lamarin ya farune a unguwan Tiv, Lugbe a babban birnin tarayya, Abuja.

 

Matasan yankin sun bi masu gwangwan din inda suka kashe 3 daga cikinsu sannan suka sakawa yar bukkatar da suke kwanciya a ciki wuta, hakanan rikicin ya rutsa da motar wani dansanda.

 

Punch ta ruwaito cewa yansanda sun kama mutane 9 da ake zargi da hannu a rikicin.

 

Me magana da yawun hukumar ‘yansandan Abuja, Azuguri Manzah ya bayyana cewa tuni aka kai wadanda ake zargi da hannu a rikicin wajan bincike kuma zaman lafiya ya dawo yankin da rikicin ya auku.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *