fbpx
Sunday, April 18
Shadow

Shugaban Majalisar Dattawa ya yi tir da sace ‘yan matan makarantar sakandaren Zamfara

 

Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya la’anci harin da aka kai ranar Juma’a a makarantar Sakandaren Gwamnati, Jangebe a Jihar Zamfara inda aka sace daruruwan ‘yan mata‘ yan makaranta.

Lawan ya nuna bakin ciki da takaicin yadda lamarin ya faru yayin da ake ci gaba da kokarin kubutar da wadanda aka sace makonnin da suka gabata a wata makarantar sakandare da ke Kagara, jihar Neja.

Lawan ya nuna juyayin sa ga ‘yan matan makarantar da aka sace sannan ya bukaci hukumomin tsaro a dukkan matakai su hada kai don tabbatar da kubutar da su cikin gaggawa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *