fbpx
Wednesday, April 21
Shadow

Sojoji sun dakile yunkurin garkuwa da Mutane akan titin Abuja zuwa Kaduna

Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana a daren jiya cewa, sojojin rundunar Operation Thunder Strike sun dakile yunkurin garkuwa da mutane akan titin Kaduna zuwa Abuja.

 

Gwamnatin jihar tace masu garkuwa da mutanen sun so su farwa matafiya a daidai Kasarami dake karamar hukumar Chukun da misalin karfe 7:38 na yamma.

 

Kwamishinan kula da tsaron cikin gida na jihar, Samuel Aruwan ne ya bayyana haka ga manema labarai inda ya baiwa matafiyan da suka samu tsaiko saboda wannan lamari hakuri. Yace kokari ne na tseratar da rayuwar jama’a da kuma dukiya.

“As at the time of this security update, traffic is flowing on both lanes of the highway, and the troops are sustaining aggressive fighting patrols to deny the criminals freedom of action,” he stated. Daily Trust.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *