fbpx
Sunday, April 18
Shadow

Sojoji sun kama mutane 9 da ake zargi da hannu a mummunan hari a kauyen Kaduna

Sojojin ‘Operation Safe Haven’ sun ce sun cafke mutum tara da ake zargi da hannu a mummunan harin a karamar hukumar Zangon Kataf da ke jihar Kaduna.

 

Kwamishinan Tsaron Cikin Gida da Harkokin Cikin Gida, Mista Samuel Aruwan ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Laraba, NAN ta ruwaito.
Aruwan ya tunatar da cewa wasu ‘yan bindiga dauke da makami sun kai hari a kauyen da yammacin ranar Lahadi.
A cewarsa, harin ya yi sanadin mutuwar mutane biyar tare da jikkata da dama.
“An kama mutane tara da ake zargi, bayan ci gaba da bin diddigin da sojoji suka yi.
“Mun kuma gano wani nau’in makamai daga kungiyar.
“A halin yanzu, an mika su ga ‘yan sanda don bincike,” in ji shi

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *