fbpx
Sunday, March 7
Shadow

Sojojin Najeriya sun kwato Marte daga Boko Haram

Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun kakkaɓe Boko Haram da ISWAP a Marte tare da ƙwato yankin da ke cikin jihar Borno.

Sanarwar da kakakin rundunar sojin Mohammed Yerima ya fiyar ranar Talata, ta ce sojojin sun ƙwato Marte ƙasa da sa’a48 na wa’adin da babban hafsan sojin Najeriya Manjo Janar Ibrahim Attahiru ya ba su.

Sanarwar ta ce dakarun wadanda suka samu taimakon sojin sama sun kashe ƴan Boko Haram da ISWAP da dama tare da lalata nakiyoyi da bama-bamai da suka dasa a yankin.

“Yanzu sojoji ke ikon yankin gaba ɗaya,” a cewar sanarwar.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *