fbpx
Sunday, March 7
Shadow

Tag: Boko Haram

Sanata Shehu Sani ya bayyana dalilin da yasa tubabbun Boko Haram ke sake komawa kungiyar

Sanata Shehu Sani ya bayyana dalilin da yasa tubabbun Boko Haram ke sake komawa kungiyar

Siyasa
Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum ya bayyana cewa Tubabbun Boko Haram na yiwa kungiyar leken Asiri a cikin jama'a sannan kuma su sake komawa cikinta.   Gwamnan ya nemi a rika yankewa 'yan Boko Haram din hukunci kawai idan an kamasu.   A martaninsa ga wannan lamari, Tsohon sanata me wakiltar Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa, yana baiwa mutane dalilin da yasa 'yan Boko Haram da suka tuba ke sake komawa kungiyar shine Jini ya fi ruwa Kauri.   https://twitter.com/ShehuSani/status/1367772434166865920?s=19    
Jama’a sun tsere yayin da Boko Haram suka kai hari Dikwa

Jama’a sun tsere yayin da Boko Haram suka kai hari Dikwa

Tsaro
Jama'ar gari sun yi ta kansu yayin da Boko Haram suka kai hari garin Dikwa na jihar Borno.   Wata majiya ta shaidawa Daily Trust cewa Boko Haram sun shiga garinne da Misalin karfe 6:30 na yamma ranar Litinin inda suke ta harbin kan mai uwa da wabi.   Saidai Sojojin sama dana kasa sun dakile harin Boko Haram din.  Wata majiyar tsaro ta tabbatar da faruwar Lamarin.
Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau ya fitar da Bidiyo inda yayi magana akan harin Borno

Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau ya fitar da Bidiyo inda yayi magana akan harin Borno

Tsaro
Kungiyar Boko Haram ta ɗauki alhakin harin da aka kai Maiduguri babbaan jihar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya da yammacin ranar Talata. A wani bidiyo da BBC ta gani, wani mutum da ke iƙirarin shi ne shugaban ƙungiyar Abubakar Shekau ya nuna jin dadinsa game da kai harin da ya ce sun samu nasara. Ba a ga fuskar Abubakar Shekau a zahiri yana magana a cikin bidiyon na minti biyar ba, amma ana iya jin muryar da ke ikirarin shi ne a karkashin bidiyon wasu mutane da ke harba rokoki a cikin wani yanki. Mai maganar ya nanata irin kyamar da kungiyar ke yi wa ga tsarin ƙasashen yammacin duniya, sannan ya sha alwashin kafa daular musulunci. A farkon wannan makon wasu makamai suka dira a wata unguwa da ke da yawan jama'a a babban birnin Maiduguri tare d...
Graphic: Hotunan gawarwakin ‘yan Boko Haram da yawa da Sojojin Najeriya suka kashe a harin da suka kai musu

Graphic: Hotunan gawarwakin ‘yan Boko Haram da yawa da Sojojin Najeriya suka kashe a harin da suka kai musu

Tsaro
Sojojin Najeriya sun kaiwa Boko Haram hari a garin Marte dake jihar Borno inda suka kashe 'yan kungiyar da dama.   Sojojin kasa dana Sama ne suka yiwa Boko Haram Luguden wutar. Banda Marte kuma Sojojin sun yi irin wannan kisan na 'yan Boko Haram a garuruwan Kerenoa, Chukun Gudu, Duma Kura, Duma Gana, da wasu sauran Kauyuka a Borno.   Hakanan sojojin sun lalata motocin yakin Boko Haram da kuma kwace makamai da dama. https://twitter.com/jarmari01/status/1364867454825037831?s=19   Nigerian Troops supported by Air Task Force & MNJTF have successfully cleared insurgents from Marte, Kerenoa, Chukun Gudu, Duma Kura, Duma Gana & other villages in Borno State. Several terrorists neutralized, gun trucks destroyed, & large cache of weapons recovered. ...
Dan Boko Haram ya dirkawa babban Kwamandan kungiyar da wasu da dama harsashi suka mutu bisa kuskure

Dan Boko Haram ya dirkawa babban Kwamandan kungiyar da wasu da dama harsashi suka mutu bisa kuskure

Tsaro
Wani dan Boko Haram bangaren kungiyar ISWAP da ya kware a wajan iya harbi ya kashe babban kwamanda a kungiyar da wasu 4 bisa kuskure.   An kashe kwamandan me suna Ba'ana Okocha a wani wajan kungiyar ISWAP din dake da matukar hadari me suna Arinna Sorro.   Wajan ne ISWAP ke ajiye makamanta da kuma mayakanta dake zuwa daga kasashen waje dan taimaka mata da yaki.   Maharbin ya kuskure Ba'ana da mayakan Abubakar Shekau da basu shiri da ISWAP inda kuma nan take ya bude musu wuta. Eonsintelligence ta ruwaito cewa Ba'ana ne ya jagoranci kai harin Marte da kungiyar ta kwace garin gaba daya.   Saidai daga baya, Sojojin Najeriya sun kwato Marte bayan gumurzu da aka sha sosai.  Ana ci gaba da samun baraka a tsakanin Kungiyar Boko Haram data ISWAP. Th...
Bidiyon yanda hare-haren Boko Haram suka kasance a Borno

Bidiyon yanda hare-haren Boko Haram suka kasance a Borno

Tsaro
Da yammacin jiyane aka samu hare-haren Boko Haram a Birnin Maiduguri na jihar Borno inda suka harba makamai cikin garin da suka kashe mutane akalla 10.   Saidai sojojin Najeriya sun dakile harin.   Wasu daga cikin Bidiyon lamarin sun bayyana a shafukan sada zumunya kamar haka.   https://twitter.com/ModuBodai/status/1364381150286917632?s=19   https://twitter.com/femmtye/status/1364340357840986115?s=19   https://twitter.com/Osomhenjr10/status/1364368830831742976?s=19    
Sojojin Najeriya sun kwato Marte daga Boko Haram

Sojojin Najeriya sun kwato Marte daga Boko Haram

Tsaro
Rundunar sojin Najeriya ta ce dakarunta sun kakkaɓe Boko Haram da ISWAP a Marte tare da ƙwato yankin da ke cikin jihar Borno. Sanarwar da kakakin rundunar sojin Mohammed Yerima ya fiyar ranar Talata, ta ce sojojin sun ƙwato Marte ƙasa da sa’a48 na wa’adin da babban hafsan sojin Najeriya Manjo Janar Ibrahim Attahiru ya ba su. Sanarwar ta ce dakarun wadanda suka samu taimakon sojin sama sun kashe ƴan Boko Haram da ISWAP da dama tare da lalata nakiyoyi da bama-bamai da suka dasa a yankin. “Yanzu sojoji ke ikon yankin gaba ɗaya,” a cewar sanarwar.
Kazamin fada na ci gaba da aukuwa tsakanin ‘yan Boko Haram suna ta kashe juna

Kazamin fada na ci gaba da aukuwa tsakanin ‘yan Boko Haram suna ta kashe juna

Tsaro
Fadan nuna Karfin iko tsakanin Kungiyar ISEAP data balle daga Boko Haram da kuma Boko Haram din na ci gaba da wakana.   ISWAP ta kaiwa Boko Haram hari a kauyen Sunawa dake kan iyakar Najeriya da Nijar wanda hakan yasa aka yi kazamin fada sosai.   ISWAP din ta kai harinne dan kwace wasu da aka yi garkuwa dasu da suka hada da ma'aikatan Agaji da 'yanmatan Chibok da kuma Leah Sharibu.   Kakakin Sojojin Najeriya,  Janar Muhammad Yerima ya tabbatar da wannan fadan inda yace ya farane bayan da ISWAP ta sace wasu mata dake da alaka Boko Haram.   Ya kuma tabbatar da lalata gonar Shugaban Boko Haram,  Abubakar Shekau.   The army spokesman said that the military would continue to dismantle all logistics and operational bases of the insurgents al...
Bidiyon Shugaban Sojojin Najeriya yana karfafa Musu Gwiwa su yaki Boko Haram ya sha yabo sosai

Bidiyon Shugaban Sojojin Najeriya yana karfafa Musu Gwiwa su yaki Boko Haram ya sha yabo sosai

Tsaro
Shugaban Sojojin Najeriya, Maj Gen i Attahiru ya je Borno inda ya isarwa da sojoji sakon Shugaba Buhari na jinjina.   A wani Bidiyon sa da ya watsu an ji yanda yake baiwa Sojojin Umarnin su je su yaki Boko Haram inda yace ya bada awanni 48 a kwato inda aka kaiwa Sojojin hari.   Kalaman da yayi a wajan yasa 'yan Najeriya da dama suke ta yaba masa inda har wasu ke cewa yafi tsohon shugaban sojojin da yayi Murabus, Janar Tukur Yusuf Buratai.   https://twitter.com/DejiAdesogan/status/1363558509313478657?s=19   https://twitter.com/MalaTujjani73/status/1363753914944921601?s=19