fbpx
Friday, March 5
Shadow

Tag: Coronavirus/COVID-19

Coronavirus: Sadio Mane ya bai wa Senegal tallafin £41,000

Coronavirus: Sadio Mane ya bai wa Senegal tallafin £41,000

Wasanni
Dan wasan Liverpool dan kasar Senegal Sadio Mane ya bayar da gudunmawar £41,000 ga kwamitin da kasarsa ta nada domin yaki da cutar coronavirus. Dan wasan ya dauki matakin ne bayan da ya lura da yadda cutar ke yaduwa da kasar ta Senegal. A wani bidiyo da ya wallafa a shafukan sada zumunta, Mane ya yi kira a dauki batun yaduwar cutar ta coronavirus da "matukar muhimmanci." Dan wasan ya bai wa magoya bayansa shawara kan matakan da za su dauka domi kare kansu daga kamuwa da cutar, kamar "wanke hannu tsawon dakika 30". Kawo yanzu, an tabbatar da mutum 27 da suka kamu da Covid-19 a Senegal, ko da yake biyu dsaga cikin su sun warke, a cewar ma'aikatar lafiyar kasar. BBChausa.
Hukumar hisba ta jihar kano ta gano maganin cutar coronavirus

Hukumar hisba ta jihar kano ta gano maganin cutar coronavirus

Uncategorized
Hukumar hisba ta Jihar kano tace ta gano maganin cutar corona da ta addabi duniya.   Babban kwamandan hukumar shiekh Haroun Ibn Sina ne ya bayyana hakan ta cikin wani sauti da ya wallafa a shafinsa na Facebook a jiya litinin.   Ibn Sina yace "Babban maganin cutar Coronavirus shine komawa ga Allah ta hanyar neman gafara da yawaita istigfar da bin Allah sau dakafa.   Haka zalika kwamandan yace "Abinda ya jawo wannan cuta shine yawan sabon Allah da kuma rashin bin dokokin Allah da al'umma basayi.   Sannan shiek ibn sina ya kara da Jan hankalin mutane kan suyi watsi da duk wasu bayanai na jita jita da ake yadawa kan suyi amfani da tafarnuwa ko albasa wai dan maganin cutar coronavirus.   Rahotan da Hutudole ya tattara ya gano cewa tun bayan...
Kocin kwallon kafa na farko ya mutu a dalilin Coronavirus/COVID-19 a Spain

Kocin kwallon kafa na farko ya mutu a dalilin Coronavirus/COVID-19 a Spain

Wasanni
Francisco Garcia ya kasance wani coach a Malaga a wani kulob mai suna Athletico Portada Alta.wanda bai san asalin cutar dake damun shi ba, amma daya je asibiti da alamomin cutar coronavirus sai suka ce mai cutar daji ce. Dama ya sha wahalar ciwon sankarar bargo.   An samu labarin daga wata jarida ta Spain mai suna Malaga hoy suna cewa, ayayin da Garcia yake yin numfashi dakyar an bashi shawara ya kara komawa asibiti. Bayan yaje sai aka ce mai yana da Covid-19 da ciwon huhu. Kuma ance ciwon sankarar bargo ce ta karawa coronavirus din karfi har tai ajalin shi. Masana a bangaren cututtuka sun ce da'ace bai sha wahalar cutar sankarar bargo ba zai iya tsira daga cutar Covid-19. Yan kungiyar shi sun ce, muna mika sakon ta'aziya ga yan uwa da abokan arziki na koch din mu da yatafi...
An samu me dauke da cutar  Coronavirus/COVID-19 na 3 a Najeriya

An samu me dauke da cutar Coronavirus/COVID-19 na 3 a Najeriya

Uncategorized
Jihar Legas ta sanar da cewa an samu mutum na 3 dake dauke da cutar Coronavirus/COVID-19 a Najeriya.   Wanda aka samu da cutar wata matace 'yar Najeriya me kimanin shekaru 30 data dawo daga kasar Ingila.   Shafin Twitter na ma'aikatar Lafiya ta jihar Legas din ta tabbatar da wannan lamari inda  ya bayyana cewa yanzu haka matar tana Asibiti dan kula da lafiyarta.   https://twitter.com/LSMOH/status/1239842260512051200?s=19
Za a gwada allurar riga-kafin Corona a karon farko a Washington

Za a gwada allurar riga-kafin Corona a karon farko a Washington

Uncategorized
A karon farko a birnin Washington na Amurka za a gwada allurar riga-kafin cutar Corona da aka samar a kasar.   Kamfanin dillancin labarai na AP dake Amurka ya rawaito wasu jami'an gwamnatin kasar na cewa, za a gudanar da gwaji riga-kafin a Cibiyar Binciken Lafiya ta Permanente Kaiser dake Seattle inda aka tara kudin yin maganin.   Mahukunta sun ce za a yi gwajin a kan mutane 45 masu lafiya, kuma maganin ba zai janyo su kamu da cutar ba, kawai za a ga irin tasirin da yake da shi.   Mahukuntan sun ce za a dauki tsawon watanni 8 zuwa shekara 1 kafin a kammala samar da maganin cutar Corona.   Alokacinda Corona ke ci gaba da yaduwa, kasar ta fara kokarin samar da maganinta.   Alkaluman Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya sun ce kusan mutane du...
CORONAVIRUS: Masu shan taba Sigari ko shakar hayakin ta sun fi zama cikin hadarin kamuwa da cutar>>WHO

CORONAVIRUS: Masu shan taba Sigari ko shakar hayakin ta sun fi zama cikin hadarin kamuwa da cutar>>WHO

Uncategorized
Yayin da masana kimiya ke gudanar da bincike domin samun kyakkawar fahimtar cutar Coronavirus kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) ta yi kira ga mutane musamman masu shan taba ko masu shakar hayakin taba da su nisanta kansu da haka cewa busa taba da shakar hayakin ta na sa a gaggauta kamuwa da cutar.   WHO ta yi wannan kira ne bisa ga sakamakon binciken da masana kimiya suka gudanar a wuraren gwaji 55,2924 dake kasar Chana.   Sakamakon binciken ya nuna cewa dayawa daga cikin mutanen da corononavirus ta yi mummunar ko suka mutu na dauke da wasu cututtuka a jikinsu da suka hada da cututtukan dake kama zuciya, nunfashi, hawan jini, ciwon siga, daji, tarin fuka da makamantan su.   Sakamakon ya kuma kara nun cewa mutanen da suka kamu da irin wadannan cututtuka ...
Pogba ya kafa gidauniyar yaki da Coronavirus

Pogba ya kafa gidauniyar yaki da Coronavirus

Wasanni
Shahararren dan wasan Manchester United Paul Pogba ya kafa wata gidauniya don tara kudin yaki da cutar coronavirus.   Wannan cuta dai ta karade duniya, inda yanzu haka ta harbi mutane 167,000, tare da kashe dubu 6 da dari 5.   Annobar dai ta shafi harkar wasannin motsa jiki musamman kwallon kafa, inda a nahiyar Turai aka dakatar da dukkannin gasannin kwallon kafa, haka kuma aka dakatar da mahimman taruka dabam dabam.   Da yake bikin zagayowar ranar haihuwara a jiya Lahadi, inda ya cika shekaru 27, Pogba ya ce yana harin tara fam dubu 27 ne don taimakawa wajen yaki da shu’umar cutar. Pogba ya ce, yana murnar kasancewa cikin koshin lafiya a daidai lokacin da wasu ke fama da rashin lafiya, saboda haka kamata ya yi y aba da tasa gudummawar wajen nema mus...
An bar Iyakokin kasarmu bude ga Cutar Coronavirus/COVID-19 amma an kullewa Shinkafa>>Sanata Shehu Sani

An bar Iyakokin kasarmu bude ga Cutar Coronavirus/COVID-19 amma an kullewa Shinkafa>>Sanata Shehu Sani

Siyasa
Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya a majalisar Dattawa, Shehu Sani da a lokuta daban-daban yakan bayyana ra'ayinshi kan yanda ake gudanar da mulkin kasarnan yayi magana akan barin bodar Najeriya ga Cutar Coronavirus/COVID-19.   Sani ya bayyana hakane a shafinsa na sada zumunta inda ya ru uta cewa.   Iyakokin mu na bude ga Corona amma an rufewa shinkafa.   https://twitter.com/ShehuSani/status/1239558270089560064?s=19    
Hotuna: Yanda Indiyawa suka yi bikin shan Fitsarin Shanu dan neman tsari daga Coronavirus/COVID-19

Hotuna: Yanda Indiyawa suka yi bikin shan Fitsarin Shanu dan neman tsari daga Coronavirus/COVID-19

Kiwon Lafiya
Wasu mabiya addinin Hindu a kasar India sun shirya bikin shan fitsarin shanu dan neman tsari daga kamuwa da cutar nan data addabi Duniya aka kasa samo maganinta watau Coronavirus/COVID-19.   An shirya bikinne a Ranar Asabar din data gabata, kamar ganda Reuters ta Ruwaito.   Masana sun sha yiwa mutanen kasar ta India gargadin cewa Fitsarin shanu baya maganin cutar amma saboda imaninsu da tsarkin da suke ga Shanu na da shi sun ki jin wancan gargadi.     Wani me suna Om Prakash daya halarci bikin shan fitsarin daya samu halartar mutane 200 ya bayyana cewa sun dade dama suna wanka da kashin shanun dan neman tsari.   Prakash ya kara da cewa sun dade suna shan fitsarin shanu, kimanin shekaru 21 kenan suna yin haka kuma basa ...