
Da Duminsa:’Yan Bindiga sun kashe Sojoji 5 da dansanda 1 a jihar Naija
'Yan Bindiga a jihar Naija sun kashe sojoji 5 da dansanda 1 da kuma kwashe makamai a yau, 1 ga watan Afrilu na shekarat 2021.
Rahoton ya bayyana cewa lamarin ya farund da misalin 0200hrs inda 'yan Bindigar da suka fito ta yankin Kwaki, Kurebe dake Shiroro a jihar Naija suka budewa wata tawagar jami'an tsaro wuta a daidai Allawa.
Majiyar tsaro ta shaidawa hutudole.com cewa an kashe sojoji 5 a harin da kuma dansanda 1. Sun lalata motocin aikin jami'an tsaron tare da kwashe makamai da yawa suka kuma koma ta inda auka fito.
ACTIVITIES OF BANDITS, ON 01/04/2021 , AT ABOUT 0200HRS ARMED BANDITS IN THERE NUMBERS ATTACKED JTF CAMP IN ALLAWA SHIRORO LGA NIGER STATE AND OPENED FIRE ON SECURITIES 5 SOLDIERS AND ONE MOBIILE POLICEMAN WERE KILLED DURING THE. OPERA...