
Damfara aka min ta Daloli da yawa wanda ko Gwamnane akawa haka sai ya girgiza shiyasa nace zan kashe kaina amma yanzu hankalina ya dawo>>Ummi Zee zee
FITACCIYAR jaruma Ummi Ibrahim (Zee-Zee) ta bayyana wata damfarar ɗaruruwan miliyoyin naira da ta ce an yi mata a matsayin dalilin da ya sa ta ke son ta kashe kan ta.
A wani saƙon murya da ta fitar a yammacin wannan rana, Zee-Zee ta ce wani Inyamiri ne ya damfare ta zunzurutun kuɗi har naira miliyan 450 a kan harkar ɗanyen mai, shi ya sa ta ji gaba ɗaya ma zaman duniyar ya ishe ta.
Bayan sallama da ta yi tare da bayyana cikakken sunan ta, ta fara da cewa, “Na yi wannan ‘voice note’ ɗin nan zuwa ga ‘yan’uwa na ‘yan fim, ma’ana ‘yan Kannywood, domin in miƙa gaisuwa ta da kuma godiya ta ta musamman gare ku ga ƙauna da ku ka nuna min dangane da iftila’in da ya faɗa min a wannan satin, wanda har ta kai ga rai na ya ɓaci, shaiɗan ya shiga zuciya ta, na yi kuma iƙirarin ...