
Covid-19: Jihar Kano ita ce jiha da tafi yawan masu warkewa daga cutar Korona >> NCDC
An bayyana Jihar Kano a matsayin jihar da ta yi fintinkau wajen yawan adadin masu samun waraka daga cutar Coronavirus, hakan na bisa alkaluman hukumar hana yaduwar cutuutuka a Najeriya wato NCDC.
A rahoton da hukumar lafiya ta jihar ta fitar ta bayyana cewa jihar ta samu karin mutum 3 wadanda suka kamu da cutar Korona a cikin adadin mutum 152 da aka gwada, Wanda ya kawo adadin mutum 1,271 masu dauke da cutar a fadin jihar.
Haka kuma jihar ta sallami adadin mutum 1,029, tare sa samun mutuwar mutum 52.
Kamar yadda jaddawalin rahoton da hukumar ta wallafa.
https://twitter.com/KNSMOH/status/1280630714225119234?s=20
Haka zalika a wani labarin duka daga jihar Kano Maigirma Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya aike da neman amincewar Majalisar Dokokin jihar domin ...