
Mun Gamsu da hukuncin Kotu, An fasa Mukabala da Sheikh Abduljabbar>>Gwamnatin Kano
Gwamnatin Kano ta bayyana gamsuwa da hukuncin da wata kotun majistre a jihar ta yanke na hana yin muƙabala, wato zaman tattaunawa da fitaccen malamin addinin musuluncin nan dake jihar Sheikh Nasiru Kabara.
Ranar Jumma'a ne kotun ta yanke wannan hukunci, kasa da sa'a 48 kafin gudanar da muƙabalar da aka jima ana jira.
Hukuncin ya buƙaci a tsaya a kan hukuncin da kotun ta yanke tun a ranar 8 ga watan Fabrairu, wanda ya haɗar da haramtawa Sheikh Abduljabbar yin wa'azi a jihar ta Kano.
Yayin wata zantawa da BBC, kwamishinan watsa labarai na Kano Muhammadu Garba, ya ce bayan tattaunawa da gwamnati ta yi da ma'aikatar shari'a, sun gamsu da wannan hukunci, don haka an fasa yin muƙabalar da aka shirya gudanarwa a ranar Lahadin nan.
BBC ta tambaye shi a kan z...