
Gwamnatin Jihar Kebbi Ta Baiwa Sojoji Motoci 8 da Babura 20 Don Taimakawa Yakar Yan Ta’adda
A kokarin da take yi na dakile yawaitar ayyukan 'yan ta'adda, Gwamnatin jihar Kebbi ta bayar da gudummawar motocin Hilux guda takwas da babura 20 ga bataliyar sojoji ta One Brigade da ke Gusau a jihar ta Zamfara.
Sakataren Gwamnatin Jiha (SSG), Babale Umar Yauri, wanda ya mika motocin da baburan ga sabon Kwamandan Birgediya Janar Mohammed Bello Wabili, ya ce wannan shi ne kashi na farko na tallafin kamar yadda gwamnatin jihar ta kasance cikin shirin sayan karin motoci ga hukumomin tsaro.
Yauri, wanda ya ce wannan gwamnati ba ta wasa da matsalolin tsaro, ya bayyana cewa gwamnan jihar, Abubakar Atiku Bagudu ne zai iya gabatar da shi, amma ya tafi aiki wani guri.
Ya ce gwamnatin jihar ba ta takaita ga bada kayan zirga-zirga ba kawai amma ta ba da gudummawa matuka ga jaruman da s...