
Ba zamu iya lalata maboyar ‘yan Bindiga ba>>Lai Muhammad
Ministan yada labarai da Al'adu, Alhaji Lai Muhammad ya bayyana cewa sabo da kare gandun dajo da kuma kiyaye gurbatar yanayi gwamnatin tarayya ba zata iya lalata gaba dayan dazuka dan a kawar da 'yan Bindiga ba.
Ya bayyana hakane a wata hira ta Musamman da aka yi dashi inda yace amma suna kokarin ganin am kawo musu makaman da suka siya daga kasashen waje.
Yace yanzu yakin da ake na kimiyya ne kuma idan makaman suka iso Najeriya za'a yi maganin 'yan Bindigar dasu.
Yace kuma akwai bukatar hadin kai da aiki tare tsakanin gwamnoni dan kawo karshen matsalar.
We cannot destroy the forest because of climate change. The better approach is not to destroy the forest because it would affect the eco-system but what we need is better consultation with sub n...