
Hotuna da Duminsu: An yiwa Shugaba Buhari Rigakafin Coronavirus/COVID-19
Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya karbi Rigakafin cutar Coronavirus/COVID-19 da safiyar yau Asabar a Abuja.
Shima Mataimakin shugaban kasar, Farfesa Yemi Osinbajo an masa rigakafin kamar yanda shafin fadar shugaban kasar ya bayyana.
A baya dai sanarwa ta gabata cewa za'a wa shugaba Buhari da sauran manyan jami'an gwamnati rigakafin cutar Coronavirus/COVID-19 din a yau.
https://twitter.com/NGRPresident/status/1368152071401316353?s=19