Tauraron mawakin Hausa, Nura M. Inuwa ya nuna Hoton wata Masoyiyar sa da yace sunanta Hafsa.
Yace ta hadu dashi kuma saboda murna, sai da ta yi sujadar Godiya ga Allah. Nura ya kara da cewa yana mata fatan Samun Miji na gari.
Wani masoyin mawakin Fina-finan Hausa, Nura M. Inuwa ya yanka jikinsa inda ya rubuta sunan Nuran.
Nura ya saka hoton a shafinsa na sada zumunta inda yace ya gode amma banda irin haka.
https://www.instagram.com/p/CH0xjtHFyHS/?igshid=66oewnxs4pis
Nura M Inuwa, na ɗaya daga cikin mawaƙan zamani wanda za a iya cewa ya shahara a ƙasar Hausa, kuma ya yi wakoƙi musamman na soyayya da dama.
A wata tattaunawa da BBC ta yi da mawaƙin a Shafin Instagram da Facebook, mawaƙin ya bayyana cewa ya fara waƙa ne tun a 2007, kuma ya fara ne da waƙar siyasa.
A cewarsa, a halin yanzu waka ta zama sana'a, kuma hanya ce da zai iya isar wa mutane sako musamman idan ya ga ɓarna sai ya gyara.
Ya ce wakokinsa da dama sun kawo sauyi, domin akwai wata waƙarsa mai suna 'Ga Wuri Ga Waina' wadda a ciki ne ya yi magana kan makomar wanda ya kashe kansa.
Ya ce a sakamakon haka "akwai waɗanda suka kira ni suka ce na yi ceto, ma'ana na ƙwaci wata yarinya daga halaka, tana ƙoƙarin halaka kanta ta ji waƙar 'Ga Wuri Ga Waina'...