fbpx
Sunday, April 18
Shadow

Tag: Rano

Masarautar Rano ta dakatar da Dagatai 2 saboda boye tallafin Coronavirus/COVID-19 da aka basu su rabawa Mutane

Masarautar Rano ta dakatar da Dagatai 2 saboda boye tallafin Coronavirus/COVID-19 da aka basu su rabawa Mutane

Uncategorized
Masarautar Rano da ke jihar Kano ta dakatar da Dagatai guda biyu sakamakon zarginsu da ɓoye kayan tallafin korona da gwamnati ta bayar a rabawa talakawa.   Da yake bada umarnin Chiroman Rano kuma hakimin Rano Alhaji Manniru Tafida Abubakar ILa ne ya dakatar da dagatan biyu, bisa umarnin mai martaba Sarkin Rano Alhaji Muhammadu Kabiru Inuwa. Dagatan da’aka da katar sun haɗa da Umar Yusuf, wanda shi ne dagacin Zurgu da kuma Kamilu Zambur wanda ya ke a matsayin Dagacin Zambur, ana zarginsu da ƙin rabawa talakawansu kayayyakin abinci wanda gwamnati ta bayar domin ragewa al’umma radadin rayuwa tun bayan bullar tallafin korona.   Wakilin hutudole ya rawaito mana cewa tuni dai aka aike da wakilci zuwa ƙasar dagatan da abin ya shafa.