fbpx
Sunday, April 18
Shadow

Tirkashi: Masu garkuwa da mutane sun nemi fansar Naira miliyan 100 kafin su saki dalibin jama’ar Ibadan dake hannunsu

Masu garkuwa da mutane na wani dalibi a sashen ilimin zamantakewar al’umma na Jami’ar Ibadan (UI), Emmanuel Odetunde, sun nemi kudin fansa na N100m kafin su sake shi.

An sace Emmanuel Odetunde da misalin karfe 5 na yamma a ranar Litinin yayin da yake aiki a gonar kaji ta mahaifinsa dake Oke Odan, a yankin Apete na Ibadan, babban birnin Jihar Oyo.

Sai dai dan uwan ​​wanda aka sace, Samuel Odetunde, ya fada wa manema labarai cewa, masu garkuwar sun kira danginsu, suna neman fansar Naira miliyan 100 kafin su sake shi.

Samuel ya kara da cewa Lafiyar dan uwansa ta fiye masa komai amma kuma kaf danginsu baza su iya hada wadanda makudan kudade ba.

Kakakin ‘yan sanda na Jihar Oyo, Olugbenga Fadeyi, ya ce yan sanda suna aiki tare da sauran jami’an tsaro don tabbatar da cewa wanda an kubutar da dalibin ba tare da an samu wata matsala ba.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *