fbpx
Sunday, April 18
Shadow

Tsohon dan takarar shugaban kasa a karkashin Jam’iyyar APDA, Mohammed Shittu ya koma APC

Alhaji Mohammed Shittu, tsohon dan takarar shugaban kasa na rusassar jam’iyyar Advanced People’s Democratic Alliance (APDA) ya koma jam’iyyar All Progressives Congress.

Tsohon shugaban jam’iyyar APDA na kasa wanda yana daya daga cikin jam’iyyun siyasa 74 da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta soke wa rajista a shekarar 2020, ya yi rajista a Unguwar sa da ke Gwagwa a Babban Birnin Tarayya (FCT) Abuja.

Shittu ya kuma yi kira da a kafa tsarin jam’iyyu biyu a kasar wanda a cewarsa, zai taimaka wajen gina dimokuradiyya mai karfi da bunkasa rayuwar zamantakewar al’umma da tattalin arziki.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *