fbpx
Sunday, March 7
Shadow

Wasu makarantun Jihar Neja sunyi shekaru 40 ba’a masu fenti ba – Gwamna Bello

Gwamna Abubakar Bello ya bayyana cewa wasu makarantu a jihar Neja da yake mulki ba a fentin su a cikin shekaru 40 da suka gabata.

Gwamnan wanda ya yi magana da manema labarai kan kokarin da aka yi na ganin an sako daliban da mambobin Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati da ke Kagara.

Gwamna Bello ya kuma bayyana cewa makarantu 50 daga cikin makarantun gwamnati 60 da ke kananan hukumomi 25 na jihar, ba su da shinge (zagaya).

Yace akwai makarantun Jihar da sukayi kusan shekaru 40 ba’a masu fenti ba.

Gwamnan yace wannan binciken ba’a Gwamnatinsa aka fara ba, sannan kuma sai anyi kusan shekaru 20 kafin a gyara su.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *