fbpx
Sunday, April 18
Shadow

Wasu mazauna garin Aliero sun yiwa wani dalibin ajin karshe a jami’ar KSUSTA duka har lahira, bisa zarginsa da yiwa wakilin POS zamba

Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Jihar Kebbi dake Aliero ta ba da umarnin rufe ma’aikatar ba tare da bata lokaci ba bayan kisan gillar da wasu mazauna Aleiro suka yi wa wani dalibin shekarar karshe dake karatun Biochemistry.

An bayyana cewa mazauna Aliero sun lakadawa dalibin duka har lahira sakamakon zargin da ake yi masa na damfarar wakilin POS N12000.

Ance dalibin ya tura N12000 ga wakilin POS a matsayin kudin sabuwar wayarsa, don haka ya karbi wayar, amma wakilin POS din bai ga sakon shigowar kudin ba.

Wakilin POS ya yanke shawarar bashi kudin kuma ya dauki lambar wayarsa idan har akwai kuskure bayan cinikin zai nemi shi.

Bayan wasu awanni, wakilin POS din ya kira dalibin ya shaida masa cewa har zuwa wannan lokacin bai samu sakon shigowar kudin ba, dalibin ya ce masa ya jira na wani lokaci.

Daga baya sai dalilin ya samu sako daga bakin cewa kudin basu shiga asusun wakilin POS din ba, sai kawai ya koma wajen wakilin domin ya sanar da shi abunda ake ciki.

Komawarsa keda wuya, sai Wakilin POS din ya sanar da mutane cewa dalibin barawo ne kuma nan take, mutane suka taru suka fara duka shi wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwarsa.

Wani ma’aikacin jami’ar, wanda ya nemi a boye sunansa, sun tabbatar da faruwar lamarin tare da rufe jami’ar ba tare da bata lokaci ba.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sanda ta Jihar Kebbi, DSP Nafiu Abubakar, shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya tabbatar da cewa za a gurfanar da masu laifin a gaban kuliya domin har an kamasu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *