fbpx
Sunday, March 7
Shadow

Wasu ‘yan bindiga sun harbe mutum 7 a jihar Edo

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin makiyaya ne, a ranar Alhamis, sun kashe akalla mutane bakwai, hudu daga cikinsu manoma ne, a yayin da suke dawowa daga gonakinsu a Jihar Edo.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Edo, Chidi Nwabuzor, ya tabbatar da faruwar lamarin kuma ya ce, rundunar na kokari wajan kamo wadanda suka aikata aika-aikan.

Wata shaidar gani da ido da ke yankin Misis Janet Ighodaro  ta shaidawa manema labarai cewa wadanda ake zargin Makiyaya ne.

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *