fbpx
Sunday, April 18
Shadow

Wata yarinya yar shekaru 14 ta murde mazakutar kakanta sai da ya nemi agaji, bayan yayi kokarin yi mata fyade

An kama wani kaka dan shekaru 49 bayan ya kokarin yiwa jikanyarsa fyade.

An bayyana cewa lamarin ya faru ne a layin Bhekani da ke Ntabazinduna, lardin Matabeleland na Arewacin Zimbabwe a ranar 8 ga Fabrairu da misalin karfe 3 na yamma.

An ce kakan ya shiga dakin yarinya Inda ya fara shafar jikinta tare da yi mata tsirara da nufin yi mata fyade.

Daga nan sai kuwa Yarinya ta rike masa mazakuta ta matse sosai har sai da yayi kuka, ya nemi agajin jama’a.

Sai yarinya ta gudu ta barshi a kwance, kuma ta nufin wajen kakarta ta bayyana mata abunda ya faru.

A halin yanzu an kama kakan tare da gurfanar a gaban alkalin kotun Bulawayo Nomasiko Ndlovu wanda ya ba da umarnin tsare shi har zuwa ranar 23 ga Afrilu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *