An kashe mutum daya a ranar Laraba yayin da wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su wanene ba suka far wa wasu matafiya a kan hanyar Osogbo zuwa Ibokun a cikin jihar Osun.
An gano cewa ‘yan bindigar sun tare hanyar ne tare da hana ababen hawa motsawa yayin da suke harbi lokaci-lokaci.
An ce sun yi wa fasinjojin fashin kudadensu da wasu abubuwa masu muhimmanci sannan suka bar wurin bayan sun harbe daya daga cikin mutanen.
An tattaro cewa yan bindigan sun tsere kafin jami’an tsaro da aka tura su kamasu sun isa wurin.
‘Yan sanda sun kwashe gawar mutumin da aka kashe tare da ceton sauran wadanda abin ya shafa daga wurin.
An ajiye gawar mamacin, wanda ba a iya tantance asalinsa ba, a asibitin jihar da ke Osogbo.