fbpx
Tuesday, March 9
Shadow

‘Yan bindiga sun kashe basaraken gargajiya a jihar Ondo

Wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu satar mutane ne a yammacin ranar Alhamis sun harbe wani basaraken gargajiya Oba Israel Adeusi a jihar Ondo.

Basaraken, wanda rahotanni su ka bayyana cewa, ya dawo ne daga Ifure zuwa Akure bayan wata ganawa. ya yin da ya ci karo da shingen masu satar mutane a yankin Elegbeka lokacin da lamarin ya faru.

An rawaito cewa direban nasa ya yi kokarin juyawa don kauce wa masu garkuwar a lokacin da suka harbi motarsu wanda sanadin hakan harsashi ya samu basaraken.

Bayan an garzaya dashi ne zuwa Asbiti  rai yayi halin nasa.

Wata majiya ta bayyana wa jaridar Tribune  cewa gwamnan jihar, Mista Rotimi Akeredolu, a lokacin da ya samu labarin faruwar lamarin ya garzaya Asbitin da aka kwantar da basaraken inda aka tabbatar masa da mutuwarsa.

 

 

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *