Wasu ‘yan bindiga sun kai hari tare da harbe wani dan sanda a jihar Delta.
Jaridar DAILY POST ta tattaro cewa lamarin ya faru ne kusa da sabon yankin Hukumar Kula da Tashoshin Jiragen Ruwa na Najeriya, NPA a Warri.
Maharan sun tafi da bindigarsa AK-47.
An gano cewa mamacin yaje rakiyar abokin shi ne lokacin da ‘yan bindigar suka kashe shi. Hutudole ya ruwaito muku cewa, Lokacin da aka tuntube shi don jin ta bakin, Jami’in Hulda da Jama’a na ’Yan sandan Jihar Delta, DSP Onome Onovwakpoyeya, ya tabbatar da rahoton a wani sakon tes.
Sakon rubutu ya ce “Ee, kuma wannan labarin ne labarin kawai”.