Yan bindiga sun kashe Zaharadeen Sani Tsafe (Sani Na Indo) tare da’ ya’yansa maza biyu a kauyen Gilla da ke karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara.
Rahotannin sun bayyana cewa, yan bindigar sun afka gidan Sani Na Indo a daren Asabar, 27 ga Fabrairu suka kashe shi tare da kananan yara biyu.
An gudunar Jana’izarsu tare da binne gawarwakinsu a safiyar ranar Lahadi.