fbpx
Sunday, April 18
Shadow

Yan bindiga sun kashe yan sanda 4 a Jihar Kuros Ribas

Wasu yan bindinga sun kashe yan sanda 4 wadanda suke bakin shingen binciken jami’an tsaro a kan hanyar Idundung a wajen karamar hukumar Calabar, Jihar Kuros Ribas.

A cewar mazauna yankin da ake kira Ayan-Mbat community, lamarin ya faru ne da misalin 1 na daren Alhamis.

Kwamishinan ‘yan sanda a jihar, CP Sikiru Kayode Akande ya tabbatar da afkuwar lamarin.

Yace; makasudin mutanen shine su sanyaya zukutan mu, amma muna nan da karfin gwiwa kuma za mu mayar musu da martani.

Ya kara da cewa sau da yawa ana cewa, wanda ya yi dariya ta farko shi zaiyi ta ƙarshe ya fi dariya; don haka mutanen Kuros Riba su jira wannan dariya ta ƙarshe su gani.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *