fbpx
Wednesday, April 21
Shadow

‘Yan Boko Haram na rige-rigen mika wuya, shekau ma zai mika wuya kwanannan, An kashe Boko Haram 13>>Hukumar Soji

Rundunar sojin Najeriya ta dakile harin da mayakan Boko Haram Suka yi yunkurin kaiwa a garin Gaidam na jihar Yobe a jiya,Litinin.

 

Rahotanni sun bayyana cewa,Boko Haram din basu ji dadadi ba a hannun sojojin na rundunar Operation Lafiya Dole inda suka hanasu cimma burinsu na kaddamar da hari a Geidam.

 

Rahotan yace an kashe ‘yan Boko Haram din su 13, sannan an kwato bindigogi  AK47 guda 6 da motocin yaki 2.

 

Babu dai soja ko daya da aka kashe a harin.

 

Hakanan hukumar sojin ta bayyana cewa, nan gaba kadan shugaban kungiyar ta Boko Haram, Abubakar Shekau zai mika wuya saboda bashi da gurin Buya.

 

Hakanan me magana da yawun hukumar tsaron,Majo Janar John Enenche ya bayyana cewa akwai mayakan Boko haram din da dama dake mika wuya.

Ya kara da cewa idan suka yi saranda za’a karbesu haka dokar yaki ta kasa da kasa ta tanada.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

1 Comment

  • Abdu abba

    Personally, I comment the effort of our gallant soldiers, this is what we have been expecting long ago.. Go ahead Allah will saw you through.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *