Gwamnan jihar Nasarawa, Abdullahi Sule ya bayyana cewa mayakan Boko Haram na taruwa dan kaiwa mutane hare-hare.
Ya bayyana hakane bayan ganawar da yayi da shugaban kasa,Muhammadu Buhari a fadarsa dake Abuja.
Saidai ya bayyana cewa, bayan ganawa da shugaba Buhari ya samu yakinin cewa, za’a yi maganin matsalar.