Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Zamfara, Abutu Yaro ya bayyana cewa kimanin‘ yan mata 317 ne yan bindinga suka sace daga makarantar sakandaren ilimin mata ta Jangebe da ke jihar Zamfara, a safiyar yau 26 ga Fabrairu.
Kwamishinan ya ce tuni aka fara aikin bincike domin kubutar da daliban 317 da ‘yan bindigan suka sace.
Kwamishinan ‘yan sandan ya kuma bayyana cewa, Kwamandan rundunar Hadarin Daji, da Manjo Janar Aminu Bande, da Birged ta daya Brigade, da rundunar sojojin Nijeriya ta Gusau, da sauran jami’an gwamnatin jihar sun jagoranci wata tawaga mai dauke da muggan makamai zuwa Jangebe don taimakawa wajen ceto daliban.
Ya yi kira ga iyayen yara da jama’a da su kwantar da hankalinsa domin hadin gwiwar ‘yan sanda da sauran jami’an tsaro zai taimaka wajen nasarar ceto daliban.