fbpx
Sunday, April 18
Shadow

‘Yan Najeriya duk abinda zaka musu basu godewa, Sau 3 Ina tsallake harin kwantan Baunar Boko Haram>>Tsohon Shugaban Soji, Janar Tukur Yusuf Buratai

Tsohon Shugaban Sojojin Najeriya,  Janar Tukur Yusuf Buratai ya bayyana cewa, ‘yan Najeriya basu da godiyar Allah.

 

Yace duk kokarin yaki da ta’addanci da yayi lokacin yana shugaban Sojojin Najeriya mutane basu gode ba.

 

Buratai ya bayyana hakane a wajan wani taro da aka yi a jihar Osun dan karramashi. Da yake magana ta bakin wakilin daya tura wajan taron, Buratai yace zau 3 yana tsallake harin kwatan Baunar da Boko Haram ke kai masa.

 

Saidai yace zai ci gaba da bayar da Gudummawa duk da yake yayi Ritaya iya iyawarsa.

 

“At the war front, many things happened and Nigerians are not appreciative. Three times I was ambushed and jumped into the bush with my men and engaged the insurgents. My relationship with Olowu of Kuta is divine,” Buratai said.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *