fbpx
Sunday, April 18
Shadow

Yan Sandan Sun Kama Wasu Mutane 4 Da Sama Da Naira Miliyan 5.7 Na Kudin Bogi a Abuja

Rundunar ‘yan sanda reshen babban birnin tarayya (FCT) ta samu nasarar cafke wasu mutane hudu da ake zargi da mallakar jabun kudi miliyan N5.7 a Gundumar Wuye.

A cikin wata sanarwa, mai magana da yawun rundunar, ASP Maryam Yusuf, ta ba da sunayen wadanda ake zargin kamar haka; Kamal Haruna, Frank Onoja, Adejoh Stephen da Guede Nelson.
ASP Yusuf ta ce wadanda ake zargin, a yayin da ake yi musu tambayoyi, sun amsa cewa sun yi amfani da takardun kudin ne wajen damfarar mutane.
Ta kuma ce jami’an ‘yan sanda daga Galadimawa sun cafke mutum biyu da ake zargi, Charity Timothy da Sunday Godwin, a kan hanyar Durumi domin yin fashi da makami.
A cewar ta, wadanda ake zargin sun amsa laifin su na tsoratar da mazauna Durumi, sannan ta kara da cewa an kwato wata karamar motar Volkswagen Golf mai lamba BWR 903 HE daga hannun su.
Ta kara da cewa mambobin wasu gungun ‘yan fashi da makami su bakwai sun kuma kama su a Kafe-Life Camp a yayin sintirin da suka saba.
Ta yi kira ga mazauna yankin da su kai rahoton duk wani motsin da ba su yarda da su ba ta hanyar lambobin gaggawa ko matsala : 08032003913, 08061581938, 07057337653 da 08028940883.
Ta kuma bukaci mazauna yankin da su kai rahoton rashin da’a daga duk wani jami’in dan sanda ta hannun ofishin koke-koken Jama’a (PCB) – 09022222352.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *