fbpx
Sunday, March 7
Shadow

Yanda Sojojin Najeriya Suka Kashe ‘Yan Bindiga 80, Tare Da Kubutar Da Wasu Mutane 17 Da Aka Sace

Dakarun rundunar operation Sahel Sanity a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya sun kashe maharan 80, sun gano bindigogi 7 da shanu 943, in ji Daraktan yada labarai na rundunar tsaro, Birgediya Janar Benard Onyeuko ya bayyana a ranar Asabar.

“Dakarun kwantar da tarzoma na Operation Sahel Sanity, sun gudanar da jerin gwanon ayyuka, kwantan bauna da sauran sintirai a cikin jihohin Sakkwato, Katsina da Zamfara.
“Wadannan aiyyukan sun haifar da kwato wadanda aka sace, dawo da shanun da aka sace, kame wasu da ake zargi da yin garkuwa da mutane, kame wasu‘ yan bindiga da kuma masu basu bayanai.
“Ya zuwa yanzu, a cikin dukkan ayyukan da aka gudanar, an kashe yan bindiga guda 80, an kwato shanu 943, an kubutar da tumakai 633; An kama wasu ‘yan bindiga da ake zargi guda 33; An gano bindigogi kirar AK47 guda 7, kirar GPMG guda 1 da bindigogi kirar Dane guda 16; An kubutar da wadanda aka sace 17 tare da kama wasu masu bada bayanai da aiki da yan bindiga guda 14.
Ya kara da cewa, sansanonin ‘yan bindiga da dama ciki har da sananniyar Dangote Triangle da sansanonin kayan aikinsu, sojojin Operation SAHEL SANITY sun lalata su.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *