Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya sauke mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Salihu Tanko Yakasai daga nadin da aka yi masa.
Kwamishinan yada labarai, Malam Muhammad Garba, wanda ya sanar da umarnin na gwamnan ta hanyar wata sanarwa a ranar Asabar, ya ce korar ta dogara ne da “maganganun da Yakasai ke ci gaba da yi ba tare da kulawa ba da kuma kalaman da ake ganin sun saba wa matsayin gwamnatin All Progressive Congress (APC).
A cikin maganganun na shi yace Shugaba Buhari da Gwamnonin APC sun gaza sauke nauyin da ke kansu musamman wajen kare rayukan da dukiyoyin al’umma, ya kara da cewa su gyara ko suyi murabus.