Gwamnan Jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, ya ba da umarnin rufe dukkan makarantun kwana da ke wajen garin Sakkwato saboda munanan matsalolin tsaro a jihar da yankin Arewa maso Yammacin kasar.
Sakataren gwamnatin jihar, Malam Sa’idu Umar, wanda ya bayyana hakan yayin taron majalisar tsaron jihar a ranar Lahadi, ya ce rufewar ya fara aiki ne nan take daga Litinin, 1 ga Maris kuma zai kasance har zuwa wani lokaci, har sai an samu sauki a matsalar tsaron da ya addabi jihar a ‘yan kwanakin nan.
Umar ya kara da cewa wannan umarnin ba zai shafi makarantun kwana da ke cikin garin Sakkwato ta Arewa, Sakkwato ta Kudu, Bodinga da Wamakko.