fbpx
Tuesday, March 9
Shadow

Yanzu-Yanzu: Hukumar NAFDAC ta amince da allurar AstraZeneca a matsayin rigakafin COVID19 a Najeriya

Hukumar Kula da Abinci da Magunguna a Najeriya (NAFDAC), ta amince da allurar Oxford / AstraZeneca a matsayin rigakafin COVID19 da za’ayi amfani da ita a Najeriya.

A wani taron manema labarai da aka gudanar da safiyar yau 18 ga watan Fabrairu, Darakta-Janar na NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye, ya ce hukumar ta karbi allurar ne mako guda da ya gabata, kuma kwamitin NAFDAC sunyi gwagwajen domin sannin inganci da kuma illar allurar, kuma a karshe sun gano cewa allurar zatayi tasiri sosai ga yan Nageriya ba tare da wata illa ba.

Adeyeye ya ce za a iya adana maganin a matakin digiri 2 zuwa 8, ya kara da cewa akwai karin alluran riga-kafi guda uku da ke kan gwaji, amma binciken da aka yi kan Astrazeneca ya nuna cewa amfani da allurar zaiyi tasiri sosai wajen dakile kamuwa daga cutar Covid-19.

Ana sa ran Najeriya za ta soma yiwa mutane rigakafin COVID19 a karshen watan Fabrairu.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *