fbpx
Sunday, April 18
Shadow

Zaa bada Tukwicin 150,000 ga duk wanda ya gano jabun magunguna a jihar Kano

Hukumar Kula da Hakkin mai Saye da Sayarwa ta jihar Kano (Consumer Protection Council) KSCPC ta sami nasarar kama wasu jabun magunguna na sama da Naira Miliyan Dari da hamsin (N150).

 

A wata takardar da ya rabawa manema labarai yau a a kano, Jami’an hurda da jamaa na hukuma Nabilisi Abubakar Kofar Na’isa ya bayyana cewa.

 

Mai rikon Shugaban Hukumar Kula da Hakkin mai Saye da Sayarwa ta jihar Kano Hon. Dr. Baffa Babba Dan’agundi ne ya bayyana haka, jim kadan bayan samun nasarar kama jabun magunguna a wani gurin ajiyar kaya da ke Karamar Hukumar Ungogo.

 

Ya ce sun sami rahoton sirri daga wajen wani mazaunin wurin, inda ya sanar da irin hada-hadar jabun magungunan da ake aikatawa wurin, sai hukumar ta kai samame karfe 2:00 na daren jiya Laraba, kuma ta kamo su.

 

Sannan yaya ce akwai tukwaici na Naira Dubu Dari da Hamsin ga duk wanda ya kawo rahoton wurin da ake hada-hadar jabun magungunan da jabun kayayyakin amfani na yau da kullum, duka ana yi ne don kare lafiyar Al’ummar Kano.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *