Ministan kwadago da samar da ayyuka, Dakta Chris Ngige, a ranar Asabar, ya bukaci mambobin jam’iyyar All Progressives Congress (APC), a jihar Anambra, da kada su damu, game da zaben gwamna da za’a gudanar a jihar, yana mai bayar da tabbacin cewa Jam’iyyar APC ce zata karbe ikon jihar. A nan da watan Nuwamban shekarar 2021.
Ministan ya bayar da wannan tabbacin ne jim kadan bayan ya sake jaddada katin sa na zama halattacan dan jam’iyya a mazabar sa.