Shehin Malamin Addinin Islama, Sheikh Dr. Ahmad Gumi ya bayyana cewa zai kai Ziyara Kagara ta jihar Naija inda aka sace daliban makarantar Sakandare.
Ya bayyana hakane kamar yanda Daily Trust ta ruwaito inda yace yana kan hanyarsa ta zuwa Kebbi ne amma ya tsaya dan su gana da Gwamna Abubakar Bello.
Ya bayyana cewa sun gana da Gwamna Bello sosai akan matsalar tsaron.
“The governor and I spoke on several ways to deal with insecurity in a holistic manner and find solutions to the insecurity problem in the state,” he said.