fbpx
Tuesday, March 9
Shadow

Zulum Ya Bada Umarnin Daukar Karin Likitoci Ga Asibitocin Borno

Gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum a ranar Laraba ya amince da daukar karin likitoci 40.
Akwai asibitoci da dama a yankunan da ke fama da tashe-tashen hankula a jihar ba tare da likita ba.
An ba da umarnin na gwamnan ne a wani taron ganawa da manyan shugabannin gudanarwa na asibitocin gwamnati guda bakwai da cibiyoyin da ke da alaƙa da ke Maiduguri da ƙaramar hukumar Jere.
Taron wanda aka yi shi a boye, an shirya shi ne don inganta tsarin kiwon lafiya da kuma tabbatar da samar da ingantaccen aiki ga ‘yan kasa, wata sanarwa dauke da sa hannun Isa Gusau, mai ba gwamna shawara na musamman kan hulda da jama’a da kuma dabaru.
A baya, gwamnati ta amince da daukar ma’aikatan kiwon lafiya 594, daga cikin su, likitocin kiwon lafiya 86, ma’aikatan jinya 365 da ungozomomi, masu harhada magunguna 45 da kwararrun masana kiwon lafiya 100 da sauran ma’aikatan tallafi.
Gusau ya ce an gudanar da gwamnan ne a kewayen asibitin kwararru, na Maiduguri, inda ya bayar da umarnin a kara wani sashen domin magance cunkoson. Wani sashi da gwamnati ta saya, wanda ke kusa da asibitin, za a yi amfani da shi don sabon ɗakin asibitin.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:


×
Kano

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *