
Gwamnatin Tinubu ta dakatar da gina sabbin makarantun Jami’a na tsawon shekaru 7 inda tace akwai makarantun jami’a da malamai sun fi dalibai yawa
Gwamnatin tarayya ta dakatar da gina sabbin makarantun jami'a na tsawon shekaru 7.
Gwamnatin tace makarantun da ake dasu a yanzu wasu malamai sun fi dalibai yawa, wasu ma ba'a neman shigarsu.
An dauki wannan mataki ne a zaman majalisar zartaswa na ranar Laraba wanda shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya jagoranta.
Ministan Ilimi, Tunji Alausa ya tabbatar da hakan inda yace maimakon gina sabbin jami'o'in, Gwamnati zata mayar da hankali ne wajan gyara wadanda ake dasu da kuma daukar malamai kwararru.