fbpx
Wednesday, October 20
Shadow

‘Ƙone Dajin Sambisa ne kawai zai hana tubabbun ƴan Boko Haram komawa ruwa’

Wani mai sharhi kuma malami a Jami’ar Maiduguri a Najeriya ya ce ƙone Dajin Sambisa ƙurmus ne kawai abin da ya fi dacewa don hana mayakan Boko Haram da suka miƙa wuya ga gwamnati komawa ruwa.

Dakta Abubakar Othman ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa ta musamman da ya yi da sashen BBC Hausa, a daidai lokacin da ake fargabar sake komawa ruwan mayaƙan da a yanzu haka suke ta tururuwar miƙa wuya ga gwamnati da nufin sun tuba.

Mayakan Boko Haram din suna ta wannan tuba ne da ajiye makamansu bayan shafe shekara 12 ana fama da tashe-tashen hankula da kashe-kashe a yankin arewa maso gabashin Najeriya.

Malamin ya ce cikin ƙanƙanin lokaci za a iya shafe tarihin Dajin Sambisa don a hana gurɓatattu samun mafaka.

Dr Othman ya ce “lamarin nan ya daɗe, yau wajen shekara 11, yau ne gobe ne haka dai. Rayuka sun salwanta an kuma yi asarar dukiyoyi, ba zaman lafiya haka ake ta tafiya.”

Ya ce abu biyu ya kamata a duba kan wannan batu na karɓar tubabbun ƴan Boko Haram da gwamnati ke ci gaba da yi.

“Idan har su da kansu sun ce sun bari sun tuba, to abu na farko da ya kamata a yi shi ne a karbe su ɗin. A ce mun ji kun tuba mun karɓe ku, kamar dai yadda gwamnan Borno ya fada, a fara karbar tasu shi ne matakin farko.

“Don ba a son yaƙi ko ci gaba da faɗa da su. Idan sun shiga hannu an karbe su sai abu na gaba a san me za a yi a kansu.”

Mai sharhin ya ce to a nan ne gizo ke saƙar, “abin da nake nufi shi ne a tantance don gane ko tuban ne da gaske ko takura ce ta sa suka fito daga dajin suke so su sha iska su koma.

“Don haka dole ne a yi amfani da ƙwararru a fannin gano masu aikata miyagun laifuka da masana halayyar dan adam da na fannin lafiyar ƙwaƙwalwa da sauransu don yin nazari.

“A yi hira da su don gano inda suka sa gaba,” in ji shi.

Hukumomi sun ce fiye da tsofaffin ‘yan kungiyar dubu takwas ne suka mika wuya, cikinsu har da mata da kananan yara, kuma bayanai na cewa har yanzu daruruwa na ci gaba da mika wuya.

A yanzu haka dai ana killace da mutanen a wasu sansanonin hukuma a birnin Maiduguri na jihar Borno.

Sai dai masanin ya bayyana damuwa cewa idan haka kawai aka karɓe su har aka gina musu gidaje, “ni kuma su ne fa suka ƙone min gidana suka kashe min ‘yan uwa, sannan a karrama su fiye da ni ai ka ga da sauran rina a kaba,” kamar yadda ya ce.

Mai sharhin ya ce dole a sanya tababa kan lamarin, ganin sun shafe shekaru a daji suna yakar mutane kuma rana tsaka su fito su ce sun mika wuya.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *