fbpx
Thursday, December 2
Shadow

Ƙwazon ‘yan Najeriya a ƙasashen waje saboda ilimin da suka samu a gida ne>>Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ‘yan ƙasarsa mazauna ƙasashen waje na da himma sosai sakamakon tarbiyya ko ilimin da suka samu a gida kafin su fita.

Buhari ya bayyana haka ne yayin da yake ganawa da Ƙaramin Ministan Harkokin Wajen Daular Larabawa (UAE) Shaikh Shakboot Alnahyan a Faransa ranar Juma’a a gefen taron zaman lafiya da suke halarta.

A cewar wata sanarwa daga kakakin fadar shugaban, Femi Adesina, Buhari ya siffanta ‘yan ƙasarsa maza da mata a matsayin “masu gogayya a gida da waje,” kuma ya shawarce su da su ci gaba da kasancewa masu bin doka da oda.

Ya ce: “Akwai ‘yan Najeriya a ko’ina, masu ƙwazo. Kuma ƙwazon nasu na farawa ne tun daga gida (Najeriya), inda suke samun ingantaccen ilimi, su shiga sana’o’i sannan kuma su wuce ƙasashen waje.”

Haka nan, shugaban ya nemi ‘yan Najeriya “su koya wa kansu bin dokoki da tsarin ƙasashen da suke zaune a ciki ko kuma aiki”.

Yayin ganawar, Buhari ya yi maraba da shirin ƙasashen biyu na haɗin gwiwa a fannin makamashin da ba ya ƙarewa da noma da ayyukan raya ƙasa da kuma samar da rigakafin annobar korona.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *