fbpx
Saturday, December 4
Shadow

Ƴan Bindiga Sun Kashe Mutum 12 A Jihar Katsina

Wasu ‘yan bindiga ɗauke da makamai sun kashe mutum aƙalla 12 a garin Batsari ta jihar Katsina tare da raunata wasu da dama.

Maharan sun shiga garin Batsari ranar Talata da dare, inda suka dinga harbi kan mai tsautsayi.

Wani mazaunin karamar hukumar mai suna Yahaya ya shaida yadda lamarin ya faru kuma ya faɗa wa BBC Hausa cewa an yi jana’izar mutum 11 da shi.

A cewar Yahaya: “Yanzu ana ta zaman makoki a cikin gari, da ni aka yi jana’izar mutum 11 kuma na ga an taho da na 12.”

“Lokacin da suka shigo garin wasu masallatan ma ba su gama sallar Isha ba,” a cewar wani mazaunin garin daban.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Katsina, SP Gambo Isah, ya tabbatar wa BBC Hausa faruwar lamarin amma ya ce yana tsaka da tattara bayanai.

Garin Batsari na da nisan kilomita 50 daga Katsina, babban birnin Jihar Katsina, wadda ke fama da hare-haren ‘yan fashin daji masu garkuwa da mutane don kuɗin fansa.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *