fbpx
Monday, September 27
Shadow

Ɗalibai biyar na makarantar Kayan-Maradun sun kuɓuta daga hannun ƴan bindiga

Rahotanni daga jihar Zamfara ta Najeriya na cewa biyar daga cikin ɗalibai sama da 70 da ‘yan fashin daji suka sace daga wata makarantar sakandare ta Kayan-Maradun sun kuɓuta.

A jiya Laraba ne ‘yan bindiga a kan babura da motoci suka abka wa makarantar sakandaren gwamnati da ke garin Kaya a karamar hukumar Maradun suka sace ɗalibai akalla 75 da kuma malami ɗaya ana tsakiyar rubuta jarabawa.

Rahotanni sun ce ɗalibai fiye da 400 ne suke makarantar lokacin da aka kai harin.

Mahaifin ɗaya daga cikin daliban da suka tsere wadanda duk mata ne ya shaidawa BBC cewa cikin dare da misalin karfe 1 yaran suka dawo gida.

Ya ce yaran nasu sun shaida masa cewa an kasafta su gida biyu, kuma garin raba su ne suka yi nasarar kuɓuta.

Ya kuma kara da cewa yaran sun dawo cikin mawuyanci hali domin yanzu haka ana yi wa biyu daga cikinsu ƙarin ruwa a asibiti.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *