fbpx
Saturday, December 4
Shadow

Ɗan sanda na neman kotu ta kashe aurensa bisa zargin matarsa da bin maza

Wani ɗan sanda, Rafiu Ademola ɗan shekara 45 ya roƙi kotu a Igando da ta kashe aurensa da matarsa a bisa zargin ta na bin maza.

Ɗan sandan ya shaidawa kotun cewa mai-ɗakin nasa ta zama karya.

Ya kuma koka da cewa shi da idonsa ya ga irin zantukan batsa da matarsa ke yi da maza daban-daban ta WhatsApp da kuma guraren da su ke haɗuwa.

“A cikin saƙonnin da na gani har da wanda ta cewa wai ba ta da aure kuma wai a gidan yayarta ta ke zaune.

“na aika duka hirarrakin zuwa waya ta domin ya zame mini shaida,” Ademola ya shaidawa kotun.

Mai ƙarar ya ƙara da cewa matar tasa ta fiye son jiki kuma ba ta don yin girki a gidan kuma ba ta girmama mahaifansa.

A ƙarshe dai ɗan sandan ya shaidawa kotun cewa shifa yanzu ba ya son matar ta sa, inda ya roƙi kotun da ta datse igiyar auren nasu.

A na ta ɓangaren, Rashidat ta musanta duk zarge-zargen da mijin nata ya yi a kotun, amma kuma ta amince da a yanke auren.

“Ni ban taɓa bin maza ba , shine ma yanke bin mata iri-iri har ya na kawo mata cikin gidan mu na aure.

“Kwanan nan ya kore ni da ga gidan ya riƙa kuma kawo mata su na kwana a gidan,” in ji ta.

Rashidat, ƴar shekara 40 kuma mai sana’ar telanci ta shaidawa kotun cewa mijin nata ya maida ita jaka, inda ya ke jibagrta a duk sanda ya ga dama.

Kamfanin daillancin labarai, NAN ya rawaito cewa kotun, wacce ta ke ƙarƙashin alƙali Adeniyi Koledoye, ya yi kira ga ma’auratan da su zauna lafiya, inda ya ɗaga zaman zuwa 16 ga watan Disamba domin yanke hukunci.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *