fbpx
Wednesday, June 23
Shadow

Mutane 8 tare da tumakai 28 sun mutu a hatsarin mota a jihar Neja

Rundunar ‘yan sanda a Neja a ranar Talata ta ce mutane takwas da tumaki 28 sun mutu a wani hatsarin mota a kauyen Batati da ke karamar hukumar Lavun ta jihar.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Mista Adamu Usman, ya shaida wa NAN a Minna cewa wasu mutane sun samu raunuka daban-daban a lokacin da hatsarin ya faru a ranar Litinin.

Usman ya ce hatsarin ya afku ne bayan direban wata babbar mota mai lamba BG 429 KMC, ya rasa iko da motar.

Ya ce motar na dauke da tumakai 130 da kuma wasu mutane da ba a tantance adadinsu ba da ke barin Katsina zuwa Legas.

”Mutane takwas da tumaki 28 suka mutu nan take yayin da aka kwashe wasu da dama da suka samu raunuka daban-daban zuwa Babban Asibitin. Kutigi don magani.

”Mun fara bincike kuma muna gargadin direbobi da su daina daukar fasinjoji a kan motocin da aka hana.

Dan sauke manhajar hutudole a wayoyin ku. Sai a bi wannan link din na kasa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *