Sunday, 20 November 2016

Real Madrid ta lallasa Atletico Madrid da ci 3 ba ko daya: Ronaldo ne yaci duka kwallayen, yayi "hat-trick"An tashi wasan da aka buga tsakanin club din Atletico Madrid da Real Madrid, inda Real Madrid ta lallasa Atletico daci 3 da 0, kuma dan wasan nan nata me tashe, wanda ya fito daga kasar Portugal ne, wato Cistiano Ronaldo ya zura duka kwallayen, abinda ake kira da "hat-trick" a turance. Wanda hakan ya sanya wannan shine karo na 39 da ya ci kwallaye uku a wasa daya a tsawon shekaru 8 da ya yi Madrid.

No comments:

Post a Comment