Sunday, 20 November 2016

TUNATARWA:Falalar Kula Da Sallah A Kan Lokaci

Assalamu alaikum ya 'Yan uwa na musulmai maza da mata, ya kamata mu kula da sallah a tsawon rayuwarmu, saboda fadin Manzon Allah (SAW) da ya yi a wadannan hadisai...

1. Daga Abdullahi dan Umar (R. A) daga Annabi (SAW) cewa wata rana ya ambaci sallah, sai ya ce "wanda ya kiyaye ta, za ta kasance gare shi a matsayin haske, da hujja da tsira ranar alkiyama, wanda kuwa bai kula da ita ba, babu wani haske, ko hujja ko tsira da za su tabbata gare shi ranar alkiyama. Zai kasance ne tare da Karuna, Fir'auna, Hamana da Ubayyu dan Halafu. Ahmad ne ya rawaito.

2. Daga Abu katadata (R. A) daga Annabi (SAW) ya ce Allah mai girma da buwaya yace : Na farlanta wa al'ummata salloli biyar kuma na yi alkawari mai karfi cewa duk wanda ya kula da yin su a kan lokutansu zan shigar da shi Aljanna, wanda kuwa bai kula da su ba, babu wannan alkawari tsakanina da shi "Abu Dauda ne ya rawaito.

3. Daga Abu Huraira (R. A) daga Annabi (SAW) yace : Yanzu da a ce akwai wata korama a kofar gidan dayan ku wadda yake wanka a kowace rana sau biyar a cikin ta, shin kuna ganin wani datti zai wanzu a jikinsa? Sai suka ce ko kusa babu wani datti da zai yi saura a jikinsa. Sai ya ce to wannan shine misalin salloli biyar kenan wadanda Allah yake wanke zunubai da su ".

4. Daga Usman dan Affan (R. A) ya ce, Na ji Manzon Allah (SAW) yana cewa" wanda ya sallaci isha'i cikin jam'i kamar ya sallaci rabin dare ne, wanda kuma ya sallaci Asuba cikin jam'i kamar ya sallaci dare ne gaba dayanta ". Muslim ne ya rawaito.

5. Daga Abu Musal Ash'ari (R. A) cewa Manzon Allah (SAW) ya ce wanda ya sallaci Asuba da La'asar a cikin jam'i, zai shiga Aljanna. Buhari da Muslim ne suka rawaito.

Ya Allah ka bamu karfi da ikon tsaida sallah akan lokaci da kuma halarta jam'i a masallatai.

rariya

1 comment: